Kashe-kashe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 03.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kashe-kashe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Rundunar sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun bayyana cewa 'Yan bindigan sa Kai na kungiyar Seleka na tafka ta'asa a yankin arewacin kasar.

Wasu mutane da ake dangantawa da 'yan kungiyar Seleka da kuma Fulani da ke yankin arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, na ci gaba da kai hare-hare inda suka kashe akalla mutane 20, a cewar wata majiya ta sojan kasar.

Wani babban sojan Misca na Tarayyar Afirka da ke ayyukan tsaro a wannan kasa, ya shaida wa kanfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP cewar, mutanen sun kai hari a wasu garuruwa akalla goma na Markounda da ke arewa, wanda ake ganin nan gaba adadin wadanda aka kashen zai iya karuwa, ganin yadda ba'a dakatar da hare-haren ba.

Al'ummar garin Markounda dai ta watse ta bar garin yayin da wasu suka fantsama cikin dazuka, inda kawo yanzu aka tura dakarun Misca ya zuwa garin Paoua a birnin da ke makwabtaka da birnin na Markounda, inda nan ma ake kai harin. Ana zargin 'yan tsofufuwar kungiyar ta Seleka da tafka ta'asa a wannan yankin.

Mawallafi: Boukari Salissou
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe