Kasashen larabawa za su kafa rundunar tsaro ta hadin gwiwa | Labarai | DW | 29.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen larabawa za su kafa rundunar tsaro ta hadin gwiwa

Shugabannin kasashen larabawa, sun amince da ci gaba kai farmaki kan 'yan tawayen Houthis da ke Yemen, sai har sun kaiga mika makamansu.

Shugabannin sun cimma hakan ne yau a wajen shakatawa na Sharm El Sheik da ke Masar, tare da amincewa hada rundunar soji ta hadin gwiwa ta kasashen na larabawa.

Matakin na yanzu na zama wata hobbasa ce da zata zafafa farmaki kan mayakan tawayen na Houthis da ke samun tallafin kasar Iran a gwagwarmayar da su ke yi a Yemen.

A daya hannun ma, rahotanni sun ce ana ci gaba da kaiwa yan tawayen farmaki a yankunan da suke rike da su a Yemen, dakarun nan da Saudiyya ke jagoranta sun kashe 'yan tawayen 35, wasu 88 kuwa suka jikkata, kamar yadda wani jami'in ma'aikatar lafiya a yankin da 'yan tawayen ke rike da shi ya tabbatarwa kamfanin labaran Reuters.