Kasashen Koriya za su kulla kawance da Amirka
March 6, 2018Kafar yada labaran kasar ta sanar da cewar shugaba Jong Un, ya bayyana anniyar sa ta bude sabon shafin tarihin hadin kan kasashen yayin liyafar cin abincin dare a jiya Litinin. Kasashen biyu da a baya dangantaka ta yi tsami a tsakanin su, sun daidaita ne dab da fara kakar wasanin bazara na Olymphics da aka kammala a Koriya ta Kudu,
Wakilai biyar daga cikin tawagar Koriya ta Kudu wadanda su ka hada da babban mai baiwa shugaban kasar shawara akan tsaro kuma jagoran tawagar Chung Eui Yong, sun gana da kusoshin gwamnatin Koriya ta Arewa a jiya Litinin don fara shirye shiryen inganta alakar kasashen biyu da kasar Amirka. Wannan dai shi ne karo na farko da Kim Jong Un, ya gana da manyan jami'an gwamnatin Koriya ta Kudu tun shekara ta 2011 da ya hau mulki.