Kasashen duniya sun yi baki daya a sabon shirin SDGs | NRS-Import | DW | 01.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Kasashen duniya sun yi baki daya a sabon shirin SDGs

Kasashen duniya 193 suka amince da aiwatar da sabbin muradun 17 nan da shekara ta 2030.

Obama beim Gipfel zu Terrorismus im Rahmen der UN-Vollversammlung

Mahalarta taron Majalisar Dinkin Duniya

Shugabannin kasashen duniya da suka hallara a shelkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York na kasar Amirka, sun amince da sabon shirin ci-gaba mai dorewa wanda ya maye gurbin muradin karni da aka aiwatar a shekaru 15 da suka gabata, inda sabon shirin shima za a aiwatar a tsukin shekaru 15 masu zuwa.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tana cikin shuganbannin kasashen duniya da a karshen mako suka amince da sabon shirin ci-gaba mai dorewa, wanda ke da muradu 17 da wasu abubuwa kimanin 169 da sabon shirin ya kunsa.

Jamus ta bada goyon baya

Kanzlerin Angela Merkel UN Vollversammlung in New York

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

"An yi magana da yawa a kai, ba sai na kara bayani a kai ba. Abun shi ne aiwatar da jadawalin."!

Merkel ta kara da cewa wannan shiri ne da kasar Jamus ke bai wa mahimmanci, kuma wanda za a saka a gaba cikin shekaru masu zuwa.

Sabon shirin ci-gaba mai dorewar zai lashe makudan kudade wajen aiwatarwa a shekaru 15 masu zuwa kuma ya shafi kusan illahirin kasashen duniya. Kristalina Georgieva da ke zama kwamishiniyar kasafi da kula da al'uma ta kungiyar Tarayyar Turai ta nemi kasashen duniya su zage damtse kan aiwatar da sabon shirin:

Kasashen Turai na tare da shirin

"Muna bukatar masu bayar da kudaden tafiyarwa da masu aiwatarwa su tashi tsaye maimakon surutu kawai kan abin da ake bukata ba."

USA Xi Jinping und Hassan Rohani in New York

Shugaba Xi Jinping da Hassan Rohani a Amirka

Shugabannin kasashen duniya sun nuna zummar ba da makuden kudaden aiwatar da sabon shirin daga nan tuwa shekara ta 2030, ciki har da Shugaba Xi Jinping na kasar China wanda ya yi alkawarin kudade masu yawa, kuma kasar ke kan gaba wajen yawan mutane tsakanin kasasheh duniya.

Kasashen duniya 193 suka amince da aiwatar da sabbin muradun 17 nan da shekara ta 2030, yayin taro a zauren Majalisar Dinkin Duniya. Ana sa ran shirin ya rage gibin da ke tsakanin masu arziki da matalauta, da magance matsalar sauyin yanayi da wasu manyan kalubale da duniya ke fuskanta.