1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Beirut na ci gaba da karbar kayan agaji

Mahamud Yaya Azare LMJ
August 6, 2020

Adaidai lokacin da asarar rayuka da dukokiyoyin da aka tafka a hadarin abubuwa masu fashewa a kasar Lebanon ke kara bayyana, kasashen duniya na ribibin amsa rokon da shugabannin Beruit keyi, na a kai musu agajin gaggawa.

https://p.dw.com/p/3gWEl
Libanon | Gewaltige Explosion in Beirut
Wasu abubuwa masu fashewa, sun janyo asarar dimbin rayuka da dukiyoyi a LebanonHoto: Getty Images/AFP/A. Amro

Kasashen dunikyar dai na mayar da ankali wajen kai daukin kayayyakin da suka hadar da asibitocin tafi-da-gidanka da kwararru kan aikin ceto kai har ma da karnuka masu iya shanshano abun da ke karkashin barakuzai da nufin taimakawa kasar ta Lebanon, rage radadin ibtali'in da ta tsinci kanta cikinsa, sakamakon fashe-fashen da ya wakana a farkon wannan makon. Hadarin dai ya kai ga halaka kimanin mutane 140 da jikkata wasu kimanin 4.500, baya ga asarar dukiyoyin da ake kiyasta kudinsu da cewa ya kai kimanin dalar Amirka bilyan biyar.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, wanda bayan ya tura jirage uku da kayayyakin agaji ya ce zuwa da kai yafi sako, tuni ya sauka a birnin na Beirut a wannan Alhamis din, domin jajantawa da bayar da taimakon da ya ce ya dace a bayar. Jamus wacce ta ce hadarin ya lalata mata ofishin jakadancinta na Lebanon din, ita ma ta tura  tawagar kwararru domin taimaka wa mahukuntan kasar ci gaba da ceto rayukan wadanda ibtila'in ya ritsa dasu.

Libanon Macron in Beirut
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Lebanon Micheal AuonHoto: Reuters/D. Nohra

Kasashen yankin tekun Fasha ne dai ke sahun gaba wajen  amsa wannan rokon, inda jirage uku daga kasar Qatar dankare da kayayyakin agaji da magunguna gami da tarin likitoci, suka fara sauka a birnin na Beirut. Sai dai mahukuntan na lebanon sun ki karbar tayin agaji daga Isra'ila, kamar yadda Irris Merkeler ta ma'aikatar wajen Isra'ilan tai karin haske: "Munyi-munyi su karbi agaji amma sun ki. Muna tausayawa al'ummar Lebanon, kan wannan ibtila'i, kuma munso mu taimaka musu musamman wajen zakulo mutanen da ke karkashin burakuzai wanda muka kware a kai."
Shugaban Iran Hassan Rouhani  da Sarkin Jordan Abdallah Na biyu da shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune duk sun bayyana shirinsu na kwasar daruruwan masu raunuka domin yi musu magani a kasashensu.

Iran Coronavirus Präsident Hassan Rohani
Shugaba Hassan Rohani na IranHoto: picture-alliance/AA/Handout Iranian Presidency

Shugaban kasar Lebanon din Micheal Auon ne dai, ya fara fitowa karara ya nuna gazawar kasarsa wajen iya tunkarar wannan mummunan ibtila'in da ya afkawa musu, wanda har ya zuwa yanzu ba'a gama tantance yawan asarar rayuka da  dukiyoyin da aka tafka ba: "Ina godiya ga shugabannin kasashen da suka jajanta mana kan wannan mummunan balaiIn da ya afka mana. A yanzu haka kaso 80 na kayyakin more rayuwa sun durkushe a fadin kasarmu. Don haka muke magiya ga kasashen duniya da su gaggauta kawo mana dauki."

A hannu gudu 'yan kasar sun kaddamar da wani gangami mai suna "Baity Baitak," wato "gidana ai naka ne" da zimmar tarbar iyalan da ibtila'in ya raba da gidajensu da aka kiyasta sun kai dubu 300.