Kasashen duniya na ci gaba da agazawa Philippines | Labarai | DW | 13.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen duniya na ci gaba da agazawa Philippines

Kuwait ta amsa kiran da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na agaji ga al'ummar Philippines, bayan bala'in da ya afka wa kasar.

Sarkin daular Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah, ya bayar da umarnin tura agajin gaggawa da ya kai na kudi dalar Amirka miliyan 10 zuwa ga dubbannin jama'a da mahaukaciyar guguwar nan ta Hyan ta yi wa ta'adi a kasar Philippines, inda kuma ake fargabar mutuwar mutane da dama. Kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait ya ambaci ministan kula da harkokin majalisar ministoci a kasar, Sheikh Mohammad Abdullah Al-Sabah yana cewar, Ba-Saraken ya yi hakanne domin agazawa dimbin jama'ar da suka shiga cikin ukuba. Dama dai Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da asusun neman agaji na fiye da dala miliyan 300 domin tallafa wa mutanen da matsalar ta rutsa dasu. Babbar jami'ar kula da harkokin agaji na Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos, ta sanar - a birnin Manila cewar, suna bukatar kudin ne domin abinci da magunguna da samar da matsugunai ga jama'a.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Pinado Abdu Waba