1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka na bukatar dakatar da biyan basusuka

Binta Aliyu Zurmi
May 8, 2020

Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afirka ta Kudu ya ce kasashen Afirka na bukatar shekaru biyu ba tare da sun biya bashin da ake bin su ba domin farfadowa daga annobar COVID-19.

https://p.dw.com/p/3bxIP
Südafrika Präsident Cyril Ramaphosa
Hoto: AFP/M. Spatari

Bankin duniya da asusun bayar da lamuni na duniya IMF, sun goyi bayan shirin daga wa kasashen da ke da raunin tattalin arziki kafa domin samun damar fuskantar annobar coronavirus. Har ila yau sun ce masu bada bashi na kokarin bai wa nahiyar ta Afrika taimakon gaggawa na dala biliyan 57, ganin cewa wannan annobar ta bankado yadda harkar lafiya a nahiyar ke bukatar a inganta ta. 

Da yake karin bayani a taron kungiyar tarayyar Afirka da ya jagoranta, shugaban Afirka ta Kudun Cyril Ramaphosa, ya kara jaddada cewar kasashen Afirka na bukatar karin lokaci daga watanni tara da aka amince a baya zuwa shekaru biyu.

Kungiyoyin bada agaji da hukumar kasuwanci da ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya na mai kira da a yafe wa kasashen na Afirka basusukan ne maimakon dakatar da biyan na wasu shekaru.