1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

kasashe na kara kashe kudi kan makamai

Abdullahi Tanko Bala
April 24, 2023

Kasashe a fadin duniya na kashe kudade masu yawa a kan makamai yayin da yakin Rasha da Ukraine da kuma gogayyar Amurka da Chaina ke kara assasa hakan.

https://p.dw.com/p/4QUkr
USA weiter an der Spitze bei Waffenexporten/F-35
Hoto: picture alliance/dpa/dpa-Zentralbild

Muhimmin abu da za a fahimta a rahoton da cibiyar kwararru da ke nazarin zaman lafiya a duniya SIPRI ta fitar shi ne karin kashe kudade.

A shekarar 2022 masu nazarin bincike sun gano karin kashe kudi daga shekara zuwa shekara da ya karu da kashi 3.7 cikin dari da aka kashe akan makamai a duniya baki daya. Alkaluman sun nuna karuwar kashe kudin fiye da kowane lokaci. Nan Tian babban jami'i a cibiyar nazarin zaman lafiya a duniya da ke da mazauninta a Stockholm ya yi bayani da cewa

"Ko da tattalin arzikin kasashe yana bunkasa ko akasin haka, bangaren soji na cinye kaso mai yawa na kudade fiye da shekarun baya ko kuma idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, fiye da kowance a tsawon tarihi".

Bilder zu Story "Sipri Report"
Hoto: Vitaliy Belousov/SNA/imago

Ga masu bin abubuwan da ke faruwa a duniya, karin kashe kudin kan makamai bai zo da mamaki ba. gagarumin yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine ya jawo kasashen turai bai wa kasafin kudinsu na soji kulawa ta musamman. Tun daga wannan lokaci makamai masu linzami na Rasha suka rika dira biranen Ukraine. A watan Fabrairun 2022 kasashe daya bayan daya suka rika sanar da karin kashe kudade.

Kasafin kudi ga bangaren tsaro a tsakanin kasashe mambobin NATO kawancen tsaron da kasashen turai da dama ke ciki yana ta karuwa tun shekarar 2014 lokacin da Rasha ta fara kai wa Ukraine hari inda ta kwace yankin Crimea ta kuma mara  wa yan aware gabashin kasar baya. Mambobin kungiyar ta NATO sun amince su kara kashi biyu cikin dari na daukacin arzikin da kowace kasa ta ke samu a shekara har zuwa shekarar 2024.

 Nan Tian babban jami'i a cibiyar nazarin zaman lafiya a duniya ya yi tsokaci da cewa

Bilder zu Story "Sipri Report"
Hoto: Vitaliy Belousov/SNA/imago

"Ya ce ina tsammani ga kasashe da dama na turai, batu ne na yaya za a habaka dukkan bangarorin tsaro, Yawan kudaden da ake kashewa kan tsaro wata alama ce ta kashedi ga Rasha."

Gwamnatoci dai na tunkarar karin tabarbarewar tsaro ta hanyar ware makudan kudade  domin shawo kan kalubalen. Saai dai a lokaci guda alkaluman SIPRI sun nuna kudaden da ake kashewa basu kai abin da ake wallafa wa a kafofin yada labarai ko kuma a wasu lokutan yadda mahukunta suke kambamawa ba.

Yayin da ainihin abin da ake kashewa ya karu da euro triliyan biyu na karo, karon da kasashen suka tara, duk da haka ya gaza da kashi daya cikin dari idan aka kwatanta da 2013.

Tsadar farashin kayayyaki ta zama matsala babba a siyasance musamman a nan Jamus wadda a bara ta yi alkawarin zuba euro biliyan 100 kari akan kasafin kudin da ta ware ga rundunar sojin kasar domin martani ga takalar fadar da Rasha ke yi. Bayan da ta sha suka rashin zuba kudi da yawa ga fannin tsaron. Tsadar kayayyaki dai ya kassara yunkurin gwamnatin na aiwatar da manufar).