Kasar Ukraine ta rasa sojojin ta biyar | Labarai | DW | 03.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Ukraine ta rasa sojojin ta biyar

Masu goyon bayan 'yan awaren Rasha sun kashe sojin kasar Ukraine biyar

Hukumomin birnin Kiev na kasar Ukraine, sun ce an kashe sojin kasar su biyar tare da jikkata wasu 27 a wani dauki ba-dadi tsakanin magoya bayan 'yan awaren rasha dake a gabashin kasar.

Wani kakakin soji a yankin, Andriy Lysenko ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa a cikin sa'o'i 24, fada ta kazanta tsakanin sojin Ukraine din da kuma bangaren 'yan awaren na Rasha, a wani wajen da ke karkashin ikon dakarun gwamnati, a arewa maso gabashin birnin Donetsk. An dai kyautata fatar samun yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar Asabar din data gabata, lokacin da aka yi zaman tattaunawa da jami'an Ukraine da na Rasha dama 'yan aware, sai dai an tashi baram-baram.