Kasar Mali na jiran goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya | Labarai | DW | 16.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Mali na jiran goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya

Wani kuduri daga Majalisar Dinkin Duniya a kan goyon bayan matakin soji,shi ne kwai ake jira domin tura dakarun ECOWAS a Mali.

A wani taron manema labaran da ya kira,shugaban gwamnatin mali Cheik Modibo Diarra,ya bayana cewar yanzu haka komai ya daidaitui a shirye shiryen da ake yi na aikawa da dakarun kasa da kasa a yankunan arewacin kasar. Ya ce hasali ma nan da farkon makon nan ne ake saran komitin tsaro na Majalisatr Dinkin Duniya zai fitar da wani kuduri a dangane da batun. Shaugaban gwamnatin ya fadin hakan ne a gurin wani taron da aka shirya a birnin Tanger na kasar maroko. To saidai ya ce ba zai bayana dalla dalla matakan da aka dauka ba.
Tuni dai kasar faransa ta bayana goyon bayan kudurin da kungiyar ECOWAS ta dauka na shirya kimanin sojoji dubu ukku da dari biyar a wabni taron da kasashen suka kira a karshen makon jiya a Abuja Najeriya.

Mawallafi: Issoufou Mamane

Edita : Usman Shehu Usman