1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Kwango ta sanar da lokutan zabe

Mouhamadou Awal BalarabeFebruary 12, 2015

Za a gudanar da zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango a ranar 27 ga watan Nuwamban 2016 a cewar hukumar zabe mai Zaman kanta.

https://p.dw.com/p/1EaWZ
Hoto: GUY-GERVAIS KITINA/AFP/GettyImages

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango ta bayyana jadawalin zaben kasar inda ta bayana ranar 27 ga watan Nowamban 2016 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa da ma dai na 'yan majalisa. Sai dai kuma ta yi gargadin cewa bisa wasu sharuda ne zaben zai gudana, wadanda suka hada da samar ma hukumar kudin shirya zabe da kuma sabonta rejistar masu kada kuri'a

Shugaba Joseph kabila mai ci a yanzu ba shi da hurumin sake tsayawa takara bisa ga kundin tsarin mulkin jamhuriyar Demokaradiyar Kwango saboda ya riga ya yi wa'adi biyu na mulki. Sai dai kuma ana ta kai ruwa rana tsakaninsa da 'yan adawa kan take-takensa na kwaskware kudin tsarin muki domin samun damar yin tazarce.

Hukumar zaben ta Kwango ta kuma bayyana watan Oktoba a matsayin lokacin da za a gudanar da zaben kananan hukumomi, yayin da na sanataci kuwa zai gudana a watan Janairu.