Kasar Habasha ta nada sabobbin ministoci | NRS-Import | DW | 01.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Kasar Habasha ta nada sabobbin ministoci

Tayar da kayar baya da kabilun Oromo da Amhara masu rinjaye suka yi, ya sa Firayim Minista Desalegn na Habasha kafa sabuwar gwamnati domin warware rikicin kabilanci da ake fama da shi a kasar

Firayim Ministan Habasha Hailemariam Desalegn ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul bayan rikicin kabilanci da ya sa aka gudanar da zanga-zangar da aka shafe shekaru 25 ba a ga irinta ba a kasar. kabilun Oromo da Amhara da ke da kashi 60 cikin 100 na al'ummar Habasha sun zargi gwamnati da mayar da su saniyar ware, lamarin da suka ce ba zata sabu ba. Tun a watan Nowamban bara ne suka fara tayar da kayar baya domin neman sauyi, inda suka kona gine-ginen gwamnati da kanfanonin masu zuba jari na kasashen waje.

Shi dai Firayin Minista Desalegn ya raba tsiraru na kabilar Tigre da ma'aikatun harkokin waje da sadarwa domin dankasu ga 'yan kabilar Oromo masu rinjaye. Yayin da su kuma 'yan Amhara suka sami mukamin mataimakin Firayim Minista. Mata uku ne suka samu kujerar Minista a sabuwar gwamnati, yayin da tara daga cikin tsaffin ministocin suka ci gaba da rike mukamansu a sabuwar gwamnati mai membobi 30.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun nunar da cewar kimanin mutane 500 ne suka rasa rayukansu a jerin zanga-zangogin kin jinin gwamnati da kabilun Oromo da Amhara suka shafe watanni suna gudanarwa.