Kasar Habasha ta ayyana dokar tabaci | Labarai | DW | 16.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Habasha ta ayyana dokar tabaci

Kasar Habasha a ranar Juma'a ta ayyana dokar tabaci bayan da Firaminista Hailemariam Desalegn ya bayyana aniya ta sauka daga kujerarsa biyo bayan tashin hankali da rikicin siyasa da kasar ta shiga.

Äthiopien Regierung Soldaten ARCHIV (picture alliance/AP Photo/ltomlinson)

Habasha ta shiga rudani ta fiskoki da dama da suka hadar da siyasa da zamantakewa

Majalisar ministocin kasar ce dai ta Habasha ta kai ga cimma wannan matsaya ta sanya dokar tabacin a cewar hukumar yada labaran kasar ta EBC.

Kawancen EPRDF masu mulki sun gana a wannan rana ta Juma'a a cewar EBC sai dai jawaban ministocin bai fayyace tsawon wane lokaci ne dokar tabacin za ta yi aiki ba. Sama da firsinonin siyasa 600 ne dai a ka saki a kasar ta Habasha tun daga watan Janairu sai dai har kawo yanzu al'umma sun gaza gamsuwa da tafiyar da harkokin masu mulki a kasar.