Kasar Faransa ta ce bata bukatar zama a Mali
February 6, 2013Kasar Faransa a rubece ta bukaci MDD a tura rundunar kiyaye zaman Lafiya izuwa kasar Mali, da zaran sojan Faransa sun fice daga kasar ta Mali, idan al'amura suka lafa. Jakadan kasar Faransa a MDD Gerard Araud ya fadawa zauren kwamitin sulhu na MDD mai wakilai 15 da su bada izinin tura dakaru karkashin majalisar, kuma yace ya samu tabbaci daga kasashe masu wakilci, za a amince da bukatar kasar ta Faransa. Jakadan ya kara da cewa dakarun kasarsu ba za su ci gaba da kasan cewa a kasar Mali ba, don haka sai dai kawai ana bukatar dai-daituwar al'amura kafin isar dakarun na MDD. A dole ne bisa doka Kasar Mali da kanta ta bukaci a tura dakarun na MDD izuwa kasar ta, duk da cewa akwai adawa da kasan cewa dakarun ketari a tsakanin yan kasar ta Mali.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu