Kasar Eritiriya ta yi tir da harin Habasha | Labarai | DW | 13.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Eritiriya ta yi tir da harin Habasha

Dakarun kasar Habsha sun kutsa kai iyakar kasarsu da Eritiriya bayan da suka kaddamar da hari akan iyakokin kasashen biyu, lamarin da ya tayar da jijiyoyin wuya.

Gwamnatin Kasar Eritiriya ta soki lamarin makwabciyarta Habasha kan kaddamar da hari a kan iyakarta. Mazauna yankin da ke kan iyakar kasashen biyu sun shaida wa kamfanin dillancin labaru na Reuters cewar sun ta jin harbe-harben bindigogi tun a ranar Lahadi har zuwa Litinin. Wasu shaidu sun kuma bayyana cewar sun ga dakarun kasar Habasha na kutsa kai i zuwa yankin na Eritiriya.

Kawo yanzu dai, babu wani martani daga bangaren gwamnatin kasar ta Habasha a kan wannan takaddamar, to sai dai daman akwai takun saka tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna wanda yayi sanadiyar salwantar rayuka da dama a shekarun 1998 i zuwa 2000.