Kasahen kudancin Afrika zasu taimakawa Zimbabwe | Siyasa | DW | 15.08.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kasahen kudancin Afrika zasu taimakawa Zimbabwe

Kungiyar kasashen kudancin Afrika SADC ,sun shirya wani taro da zummar taimakawa kasar Zimbabwe

shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe

shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe

Shugabannin kasashe 13 na kungiyar raya kasashen kudancin Afrika SADC, zasu gana a wannan mako a kasar Botswana domin magance matsalolin da kasar Zimbabwe ta ke fuskanta.

Rushe gidajen talakawa da gudanar da kasuwanci na haram sun tunzura majalisar dinkin duniya wadda ta ce ya zuwa yanzu mutane dubu 700 ne suka rasa gidajensu a Zimbabwe wanda hakan ya tsananta matsalar rashin abinci a kasar.

Masana harkokin siyasa sun baiyana cewa wannan sabon yunkuri na diplomasiya wani babban mataki na zaben da shugaban kungiyar taraiyar Afrika Olusegun Obasnjo na Nigeria yayi wa shugaba Joachim chissano na Mozambique da ya shiga tsakani a rikicin jamiyar ZANU ta Robert Mugabe da kungiyoyin adawar kasar.

Wannan mataki dai ya nuna irin raayi da shugabannin kasashen Afrika suke da shi ne cewa tattaunawa tsakanin manyan jamiyun siyasa na Zimbabwe ita ce kadai hanya da za a bi domim magance matasalar kasar,da ada itace ke kan gaba a fannin noma a yankin kudancin Afrika sai ga shi yanzu tana fama da karancin abinci.

Ana sa ran shugaba Robert Mugabe zai halarci taron na ranar laraba da alhamis,,yana mai neman taimako da goyon baya daga abokansa domin kare kiraye kiraye da akeyi na neman sauyi a tsarin siyasar Zimbabwe.

Shugaba Mugabe dai yana fuskantar matsin lamba na kasa da kasa cewa ya shiga tattunawa da yan adawa domin nemo sabuwar hanya sahihiya da kasar zata bi,biyowa bayan rushe gidajen talakawa da ya bar dubban jamaa ba su matsuguni,yayinda kuma majalisar dinkin duniya ta yi Allah wadai da shi.

Sai dai kuma kakakin fadar shugaban kasar ta Zimbabwe George Charamba,ya baiyana imaninsa cewa shugabannin kungiyar raya kasashen kudancin Afrika SADC ba za su bi sahun sauran kasashen duniya ba wajen yin Allah wadai da shugaban na Zimbabwe.

Yace kasashen yammaci suka dauki abinda Zimbabwe tayi wani muhimmin abu amma ba haka yake ba ga shugabanin kasashen SADC,wadda ya ce suna sane da halin da kasar ta ke ciki,kuma sun san hanyar da suka dosa da zasu bullowa mataslar Zimbabwe.

Kasa da zata iya taka rawa cikin wannan matsala,cikin kungiyar kasashen kudancin Afrika it ace kasar Afrika ta kudu, wadda a yanzu take kokarin samarwa Zimbabwen rancen dala miliyan 500 muddin dai Zimbabwe ta amince ta tattauna da bangarorin da rikicin ya shafa, daga kungiyoyin kare jamaa da yan siyasa kasar.