Kasafin kudin Amirka ya janyo ce-ce ku-ce | Labarai | DW | 12.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasafin kudin Amirka ya janyo ce-ce ku-ce

Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya kaddamar da kashi biyu na kasafin kudin shekara ta 2019 tare da neman zuba makudan kudade a bangaren tsaro.

Shirin kasafin kudin na dala miliyan 4.4 wanda 'yan majalisar kasar ke yi wa kallo irin na neman shawara zai janyo suka daga bangaren masu ra'ayin rikau wadanda suke wa 'yan jam'iyyar Republican kallon masu almubazzarnci da kudi. An dai san 'yan majalisar ta Amirka da yin watsi da kasafin kudin shugaban kasa.