Karuwar wadanda suka mutu a Philippines | Labarai | DW | 22.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karuwar wadanda suka mutu a Philippines

Mahukuntan kasar Philippines sun tabbatar da mutuwar fiye da mutane dubu 5 sakamakaon guguwar da wargaza wasu sassan kasar

Hukumomin kasar Philippines sun tabbatar da mutuwar mutane dubu-biyar da dari-biyu sanadiyar mahaukaciyar guguwa ta Haiyan da ta ratsa kasar. Hukumar kula da agajin gaggawa ta kasar ta tabbatar da alkaluman.

Akwai mutane kimanin dubu 24 da suka samu raunika, sannan wasu mutanen kusan dubu-biyu sun bace. Guguwar ta kuma lalata kayan amfanin gona da duniya na kimanin dala milyan 270.

Makonnin biyu bayan wucewar mahaukaciyar guguwar ta yankunan tsakiyar kasar, har yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyukan agaji. Kuma wannan ya zama bali'i mafi muni da kasar ta Philippines ta fuskanta. A shekarar 1991 makamanciyar irin wannan guguwa ta hallaka kimanin mutane dubu-biyar da dari-daya.

Mawallafi: Sueliman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar