Karuwar wadanda suka hallaka a Tunisiya | Labarai | DW | 08.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karuwar wadanda suka hallaka a Tunisiya

Gwamnatin Tunisiya ta ce fiye da mutane 50 sun hallaka lokacin artabu tsageru masu dauke da makamai kusa da iyaka da Libiya.

Firaminista Habid Essid na kasar Tuniya ya bayyana cewar an samu karuwar addadin wadanda suka hallaka tsakanin dakarun kasar da masu matsanancin ra'ayi daga 36 zuwa mutane 55. Firaministan ya ce fararen hula bakwai, gami da jami'an tsaro 12 suna cikin wadanda suka hallaka lokacin artabun. Akwai wasu 17 da suka samu raunika.

Gwamnatin ta ce tsageru 36 suka hallaka cikin yankin kasar mai iyaka da Libiya, inda 'yan bindiga kimanin 50 suka kaddamar da hare-hare, tuni aka karfafa matakan tsaron cikin kasar. Galibin maharan sun kasance 'yan Tunisiya.