Karuwar hari kan farar hula a Ukraine | Labarai | DW | 10.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karuwar hari kan farar hula a Ukraine

Shugaba Petro Poroshenko na kasar ta Ukraine ya bayyana a yau Talata cewa wani harin makaman roka ya fada hedikwatar soji a gabashin kasar da kuma kusa da yankin da fararen hula suke.

Sojoji da farar hula sun sami raunika a harin rokar da aka kaddamar a yau Talata kan dakarun soji na kasar ta Ukraine.

Wani dan jarida mai daukar hoto ga kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa ya ga gawar wata mata bayan da makamin roka na farko ya fada yankin na Kramatorsk, garin da ke da tazarar kilomita 50 daga inda dakarun sojan kasar ta Ukraine suka ja daga dan maida martani ga mayakan 'yan awaren na Ukraine.

Ya ce akwai sojoji da fararen hula da harin ya ritsa dasu in da da damansu suka jikkata. Mahukunta a yankin Doneskt da bangaren gwamnati ke da iko da shi sun bayyana cewa an harbo makaman rokar ne daga bangaren da 'yan awaren ke da sansani a yankin Horlivka wanda ke da kimanin tazarar kilomita 50 daga Kramatorsk.

A cewar jami'in 'yan sanda mai kula da yankin akalla farar hula daya ya rasu yayin da wasu shida suka samu raunika.