1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Karuwar bukatar makamashi a Afirka

Mohammad Nasiru Awal RGB
April 13, 2021

Bukatar makamashi na karuwa a Afirka, inda yanzu haka wasu gwamnatoci a nahiyar suka karkata ga gina tashoshin samar da makamashi daga kwal.

https://p.dw.com/p/3rwxZ

Bukatar makamashi na karuwa a Afirka, inda yanzu haka wasu gwamnatoci a nahiyar suka karkata ga gina tashoshin samar da makamashi daga kwal. Sai dai masu sukar lamiri sun ce wannan gurguwar dabara ce a wannan lokaci na sauyin yanayi. Sun jawo hankali ga wasu hanyoyin da nahiyar ke da su.

Yawan dauke wutar lantarki ya zama ruwan dare yanzu a kasar Afirka ta Kudu. A da lokacin sanyin hunturu ake fuskantar matsalar daukewar wutar lantarki, amma yanzu a lokacin bazara ma matsalar ta yawaita saboda tsufa da hanyoyi da tashoshin wutar lantarkin suka yi, a daidai lokacin da bukatar makamashin ta karu. Kamar Afirka ta Kudu inda kimanin kashi 90 cikin 100 na makamashinta ke fitowa daga kwal, yanzu wasu kasashen Afirka irin su Botswana da Tanzaniya da Mosambik suna kan gaba wajen hakan kwal.

Kasashen Chiana da Rasha da Faransa suk fi ba da taikamakon kudi da na fasaha domin a gare su ya fi fa'ida a saka jari cikin harkokin da ke a kasa don fadada bangarorin tattalin arziki, masana sun ce, yanzu haka tashoshin makamashin kwal 34 a Afirka na samar da Gigawatt 53 na karfin wuta da ya yi daidai da kashi dayan bisa uku na hasken wutar lantarkin da nahiyar ke bukata. Sha tara na wadannan tashoshin makamashi suna a Afirka ta Kudu ne. Nahiyar Afirka na da dinbim albarkatun makamashi kamar iska da rana, bai kamata kudin samar da fasahar solar ya zama abin damuwa ba domin kudinsa na raguwa sosai.