Karuwar ayyukan kwadago ga yara | Zamantakewa | DW | 13.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Karuwar ayyukan kwadago ga yara

Yayin da ake makon yaki da bautar da yara a fadin duniya, a Najeriya ana samun karuwar yara da ke ayyukan kwadago musamman a shiyar arewa maso gabashin kasar da rikicin Boko Haram ya gurgunta. 

A ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara, ana hada kan gwamnatoci da kungiyoyin ma'aikata da sauran al'uma domin yin bikin ranar yaki da ayyukan kwadago da yara ke yi da nufin samar da mafita ga wannan matsalar da ke dakushe makomar yara manya gobe. Rahotanni na nuna cewa akwai akalla yara miliyan 168 da shekarunsu ya ke tsakanin biyar zuwa 14 da ke aikin kwadago a fadin duniya. Daga cikin alkamuman akwai sama da yara miliyan 15 a Najeriya da ke aikin kwadago, alkaluman su ne mafi yawan yara a nahiyar Afirka ta yamma kamar yadda kungiyar kwadago ta duniya ta bayyana.

A shiyar arewa maso gabashin Najeriya musamman dubban yara sun samu kansu cikin ayyukan kwadago da suka hada da tallace-tallace da barace-barace da tura amalanke ko Baro da Kanikanci da ma sauransu da dama. Lamarin ya kara muni ne saboda rikicin Boko Haram inda miliyoyin al'uma suka rasa matsugunansu; yara da dama kuma suka rasa iyaye lamarin da ala tilas ya sanya ba su da zabi da ya wuce ayyukan kwadago saboda su tallafawa kansu da ma 'yan uwansu.

Masu fafutukar kare hakkin yara dai na ganin bukatar samar da dokokin da za su zama katanga ga iyayen da ke da hali amma suna tura su ayyukan kwadago, wannan ma wata hanya ce ta ta rage wannan matsala.