Karshen taron Host Kohler da wasu shuwagabanin kasashen Afrika | Labarai | DW | 07.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karshen taron Host Kohler da wasu shuwagabanin kasashen Afrika

default

A daren jiya ne ,a fadar gwamnatin taraya ta Petesburg dake nan birnin Bonn, a ka kammala zaman taro da ya hada shugaban kasar Jamus Host Kohler, da wasu shuwagabanin kasashe da na gwamnatoci na Afrika.

Daga wanda su ka halarci wannan taro akwai shugaban kasar Nigeria Olesegun Obasanjo, da na Afrika ta kudu Tabon Mbeki, da praministan Habasha Meles Zenawi.

Haka zalika kurraru ta fannin ayyukan cigaban tattalin arzikin kasashen Afrika, da na kare hakokin jama´a, daga kasashen Kameru Nigeria, Niger, Zimbabwe sun kasance a taron.

A tsawon kwanaki 2 sun tantana a kan hanyoyi karfafa mu´amila da cude ni in cude ka,tsakanin Jamus da Afrika, ta hanyar cinikaya, da kywattata rayuwar al´ummomin wannan nahia da ke fama da matsaloli iri daban daban.