Karrama aikin kawar da makamai masu guba | Siyasa | DW | 11.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Karrama aikin kawar da makamai masu guba

Kwamitin Nobel ya ba da kyautar zaman lafiya ta Nobel ta shekarar 2013 ga ƙungiyar kawar da makamai masu guba a duniya wato OPCW.

Ƙungiyar hana bazuwar makamai masu guba a duniya wato OPCW ta samu lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya ta wannan shekara. A halin da ake ciki masu binciken makamai na ƙungiyar suna aikin lalata makamai masu guba na ƙasar Siriya. Ƙungiyar dai ta yi fatan cewa samun wannan kyauta zai ƙara janyo hankali ga irin aikin da take yi.

Tun a farkon watannan na Oktoba jami'an ƙungiyar wadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta dora wa alhakin lalata makamai masu guba a ƙasar Siriya, suke gudanar da wannan aiki a ƙasar da ke fama da yaƙin basasa, inda kuma a cikin watan Agusta aka yi amfani da makamai masu guba da suka hallaka fiye da dubu ɗaya.

Ƙarfafa guiwar jami'an ƙungiyar OPCW

Babban daraktan ƙungiyar ta OPCW Ahmet Üzümcü ya ce abubuwan da ke faruwa a Siriya wani gargaɗi ne da ke nuna cewaR akwai jan aiki a gaba.

Organisation for the Prohibition of Chemical Weapons (OPCW) Director General Ahmet Uzumcu speaks during a news conference in The Hague October 11, 2013. The OPCW, which is overseeing the destruction's of Syria's arsenal, won the Nobel Peace Prize, the Norwegian Nobel Committee on Friday. Set up in 1997 to eliminate all chemicals weapons worldwide, its mission gained critical importance this year after a sarin gas strike in the suburbs of Damascus killed more than 1,400 people in August. REUTERS/Michel Kooren (NETHERLANDS - Tags: POLITICS CONFLICT)

Daraktan OPCW Ahmet Üzümcü

"Kyautar zaman lafiya na zama amincewa da aikinmu wadda kuma za ta ƙarfafa mana gwiwa na ci gaba da aiki tukuru. Ina fatan cewa wannan lambar yabo da aikin da ƙungiyar OPCW ke yi hade da Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar Siriya za ta taimaka wa yunƙurin wanzar da zaman lafiya a wannan ƙasa tare da kawo ƙarshen wahalhalun da al'ummarta ke sha."

A dalilin wannan aiki ne, kwamitin ba da kyautar zaman lafiya ta Nobel dake birnin Oslo na ƙasar Norway, ya ba da lambar yabon ta wannan shekara ga ƙungiyar ta OPCW, inji Thorbjorn Jagland, shugaban kwamitin Nobel a ƙasar ta Norway:

"Kwamitin Nobel na ƙasar Norway ya yanke shawarar ba da kyautar zaman lafiya ta Nobel ta shekarar 2013 ga ƙungiyar haramta makamai masu guba ta OPCW saboda gagarumin aikin da take yi na kawar da makamai masu guba."

Kyautar ba za ta canja komai a Siriya ba

Sai dai a martanin da suka mayar 'yan adawar Siriya, ƙasar da a yanzu ƙungiyar ke aikin lalata makamai masu guba a madadin Majalisar Ɗinkin Duniya, sun ce ba wa ƙungiyar kyautar zaman lafiya ta Nobel ba zai kawo zaman lafiya a Siriya ba. Khaled Saleh shi ne kakakin 'yan adawar Siriya.

"Gaskiyar magana ita ce muna son ganin al'ummar Siriya sun samu walwala ba ma son ganin Assad ya kauce daga fuskantar shari'a. Dole a daina zubar da jini a Sirhiya, amma har yanzu gamaiyar ƙasa da ƙasa ba ta yi wani abin kirki na dakatar da zubar jinin da ke faruwa a Siriya ba. A kullum ana kashe mutane a Siriya. Ban san yadda wannan kyautar zaman lafiya za ta canja halin da ake ciki ba."

ARCHIV - Eine Medaille mit dem Konterfei von Alfred Nobel ist am 08.12.2007 im Nobel Museum in der Altstadt von Stockholm zu sehen. Die Internetseite des norwegischen Nobelkomitees und der PC eines leitenden Mitarbeiters sind seit Anfang der Woche massiven Hackerangriffen ausgesetzt, die möglicherweise aus China kommen. Vier Wochen nach der Verleihung des Friedensnobelpreises an den chinesischen Bürgerrechtler Liu Xiaobo bestätigte der Chef des Osloer Nobelinstitutes, Geir Lundestad, am Mittwoch in der Zeitung «Aftenposten», dass es einen Versuch zum Eindringen in seinen Büro-Rechner über eine fingierte Mail gegeben habe. Foto: Kay Nietfeld dpa +++(c) dpa - Bildfunk+++

Lambar yabo ta Nobel

Ƙungiyar ta da ke sa ido wajen lalata makamai masu guba a duniya an kafa ta ne a shekarar 1997, don aiwatar da yarjejeniyar sanya ido a kan makamai masu guba da aka rattaba wa hannu a ranar 13 ga watan Janerun shekarar 1993. Ya zuwa yanzu dai ƙungiyar ta sa ido wajen lalata kusan kashi 80 cikin dari na makamai masu guba a duniya.

Tuni dai ƙasashen duniya ciki har da Amirka da Tarayyar Turai suka aike da sakon taya murnar samun wannan kyauta ga ƙungiyar. Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya ce kwamitin Nobel ya yi zabi mai kyau na amincewa da namijin aikin da ƙungiyar ke yi a Siriya duk da yakin da ake yi a kasar. Shi ma shugaban hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya ce kyautar babbar amincewa ce ga muhimmiyar rawar da ƙungiyar ke takawa wajen kawar da makamai masu guba daga doron kasa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin