1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: 'Yan sanda sun kame wani mahari

Abdourahamane Hassane
March 11, 2023

'Yan sanda sun kame wani wanda ya yi garkuwa da mutane a kudancin Jamus, a cewar bayanan farko, babu wanda ya jikkata a lokacin da aka kubtar da mutanen da mutumin ya yi garkuwa da su.

https://p.dw.com/p/4OXUr
Polizeieinsatz wegen möglicher Geiselnahme in Karlsruhe
Hoto: Christoph Schmidt/dpa/picture alliance

A birnin Karlsruhe da ke kudancin Jamus 'yan sanda sun kawo karshen yin garkuwa da mutane da aka shafe sa'o'i da dama  ba tare da zubar da jini ba. A yammacin Juma'a, wata runduna ta musamman ta kai farmaki a wata kemus inda mutumin ya yi garkuwa da mutane sha daya. 'Yan sanda sun ce an kama wani matashi mai shekaru 20 da ake zargi. A cewar bayanan farko, babu wanda ya jikkata.