Karin mutuwar bakin haure kan teku | Labarai | DW | 26.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karin mutuwar bakin haure kan teku

An kara tsamo wadanda suka hallaka kan tekun Bahar Rum yayin da Italiya ta ceto bakin haure fiye da 700 wadanda suka fito daga Afirka.

Masu aikin ceto na Italiya sun tsamo bakin haure kimanin 730 kan tekun Bahar Rum tare da wadanda suka hallaka guda tara. Jami'an tsaron gabar ruwa sun kai daaki daga Jumma'a zuwa Lahadi inda suka ceto mutanen adadin da ya kai 155,000 cikin wannan shekara ta 2016. A cewar Firamnistan Italiya Matteo Renzi kasar ba za ta iya irin wannan aikin ba a shekara mai zuwa.

Fiye da bakin haure 3,500 suka hallaka kan hanyar zuwa kasashen Turai kan tekun Bahar Rum cikin wannan shekara, kamar yadda wani kiyasi na kungiyar kula da 'yan hijira ya nuna. Masu gadin gabar ruwan kasashen Turai sun ce yadda ake kai ceto kusa da gabar ruwan Libiya ya kara jefa aikin ceton cikin kasada. Kungiyar likito na gari na kowa ta ce an kara samun wadanda suka hallaka 25 a cikin tekun.