Karfafa dangantaka tsakanin Jamus da Afirka | BATUTUWA | DW | 08.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Karfafa dangantaka tsakanin Jamus da Afirka

Jamus tana kara bunkasa hulda da kasashen Afirka, inda a karshen wannan makon shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel take fara ziyarar aiki na wasu kasashe uku da ke nahiyar.

Angela Merkel ta zama shugabar gwamnatin Jamus ta farko da ta ziyarci kasar Mali. Kana lokacin ziyarar ta kwanaki uku za ta ziyarci kasashen Jamhuriyar Nijar da Habasha. Haka na zuwa lokacin da sojojin Jamhuriyar Nijar 22 suka rasa rayukansu sakamakon harin tsageru a wannan Alhamis da ta gabata. An kai harin kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Mali wadanda suka tsere daga tsagerun masu kaifin kishin addinin Islama.

Kafin fara ziyarar shugabar gwamnatin ta Jamus ta jaddada muhimmancin zaman lafiyar Tarayyar Turai ya danganta da zaman lafiya da ci-gaba a nahiyar Afirka, inda ake bukatar karin kudaden taimakin raya kasa da sabbin manufofin zuba jari da inganta harkokin gwamnati. A cewar Denis Tull na cibiyar kula da harkokin kasashen duniya da tsaro da ke birnin Berlin na Jamus yana ganin ziyarar tana da dangantaka yanayin da ake ciki.

Transallmaschine wartet auf dem Flughafen von Bamako auf die Sahara Geiseln, Mali (AP)

Ministan harkokin Jamus Jamus Frank-Walter Steinmeier cikin wannan shekara ya kai ziyara kasashen na Jamhuriyar Nijar da Mali. Duk kasashen biyu sun kasance hanyar wucewa ga bakin haure 'yan kasashen yammacin Afirka da ke neman zuwa kasashen Turai. Kana kasashen suna fuskantar kalubale daga kungiyoyin 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane da kuma masu safarar miyagun kwayoyi.

Bayan juyin mulkin shekara ta 2012 da tashe-tashen hankula sun tilasta dubban 'yan Mali hijira saboda rikicin siyasa. 'Yan ta'adda na Boko Haram daga Najeriya sun kara rikita lamura ga Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka.

Shugabar gwamnatin ta Jamus tana ziyarar kasashen na Afirka uku, yayin da kasar ta Jamus take kara taka rawa kan harkokin bunkasa zaman lafiya, kamar yadda Oswald Padonou daga gidauniyar Konrad Adenauer ke cewa sojojin Jamus da ke yankin Sahel suna gaba-gaba wajen daukaka Jamus tsakanin kasashen Afirka.

A matakin karshe Angela Merkel za ta ziyarci Habasha, inda za ta bude cibiyar zaman lafiya da tsaro ta kungiyar Tarayyar Afirka da gwamnatin Jamus ta bayar da kudaden ginin. Wannan kwanakin bayan artabu tsakanin jami'an tsaron Habasha da 'yan adawa abin da ya janyo mutuwar mutane da dama. Shugabar gwamnatin ta Jamus za ta gana da jami'an gwamnati gami da kungiyoyi masu zaman kansu domin sanin gaskiyar abin da ya faru.

Sauti da bidiyo akan labarin