Kare fararen hula a birnin Goma
July 19, 2013A saboda haka ne Majalisar ta fara tura karin dakarun yaki da za su kare birnin Goma daga mayakan 'yan tawaye. Hakan dai na zuwa ne bayan da al'ummomin yankin suka gudanar da wata zanga-zanga inda suka zargi sojojin wanzar da zaman lafiya da rashin tabuka wani abin kirki don kare su.
Kawo yanzu dai dakarun Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ba sa tsoma baki a rikicin da ake yi da 'yan tawaye, kuma suna kallo a wannan makon lokacin da mayakan kungiyar M23 suka kaddamar da sabon farmaki a kan dakarun gwamnati a kewayen birnin Goma dake zama birni mafi girma a gabacin kasar. Sai dai kakakin rundunar Majalisar Dinkin Duniya a Kongo MONUSCO, wato Martin Nesirky ya ce rundunar tana cikin damara kuma a shirye take ta tsoma baki idan fadan ya zama barazana ga fararen hula musamman a birnin na Goma.
Kare birnin Goma shi ne muhimmi
A cikin watan Maris ne Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya amince da tura karin dakaru da ya ba su ikon shiga yaki gadan-gadan musamman da 'yan tawaye. Ko shin wannan mataki da Majalisar ta dauka yanzu zai dawo da martabarta a idanun fararen hular Kongo da suka jima suna zarginta da rashin wani katabus? A hirarsu da DW kwamandan rundunar MONUSCO kuma dan kasar Brazil Carlos Alberto dos Santos Cruz ya ce abin da suka fi ba wa fifiko shi ne kare fararen hula.
"Kongo na fama da matsaloli da kungiyoyi da yawa na masu daukar makamai da suka addabi gabacin kasar. Saboda haka jama'a suka damu da a magance matsalolin. Akwai matsalolin rashin ababan more rayuwa da na hanyoyin sadarwa. Ina da tabbacin cewa za a iya magance matsalolin, amma ba a cikin dare daya ba."
Rundunar ta MONUSCO ta kunshi sojoji da ma'aikata fararen hula fiye da dubu 22 kuma ita ce wata tawaga mafi girma da Majalisar Dinkin Duniya ta taba samarwa. Yanzu haka kimanin kashi biyu bisa uku na sojojin rundunar suna a gabacin Kongo inda suke ba da kariya a ciki da wajen Goma da kuma sansanonin 'yan gudun hijira. Rundunar tana kuma horas da sojojin Kongo a game da batuuwan da suka shafi kare 'yancin dan Adam da yadda ake aiki a wuraren da ake fama da rigingimu kamar na kan iyakar Kongon da kasashe makwabtanta, inji kwamandan rundunar Carlos dos Santos Cruz.
"Matsalar gabacin Kongo ta shafi yankin gaba daya kasancewa rikici ne a kan iyakoki, saboda haka kamata yayi a warware matsalar a siyasance. A nan kuwa sojoji za su iya taimakawa. Dole ne dukkan masu hannu cikin rikicin su zage damtse idan ba haka ba haka ba zai yi wuya a gano bakin warware rikicin."
Ko da yake fadan da ake a kewayen birnin Goma ya lafa a ranar Alhamis, amma an ci gaba da zanga-zangar yin tir da Majalisar Dinkin Duniya.
A halin da ake ciki babban sakataren Majalisar ta Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya nuna matukar damuwarsa ga sabon rikicin na birnin Goma da kewayen arewacin Kivu, sannan yayi kira ga dukkan sassan da abin ya shafa da su nuna halin ya kamata kana su guji yin abubuwan da za su kara tsananta rikici tare da jefa rayuwar jama'a cikin mawuyacin hali.
Mawallafa: Marta Barroso / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas