Kara tsanantar rikicin mallakar filaye a Uganda | Zamantakewa | DW | 28.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Kara tsanantar rikicin mallakar filaye a Uganda

Manoma dake zaun a wasu yankunan kasar Uganda sun shiga wani hali mai wahala bayan da gwamnati ta kwac filayensu na noma ta sayarwa maoman Coffee na ketare.

A shekara ta 2001 ne sojin gwamnatin Uganda suka fidda kimanin mutane dubu hudu daga inda suke noma a gundumar Mubende da ke tsakiyar kasar, inda daga bisani aka saida wajen ga wani kamfani na kasar Jamus da ke noman coffee. To sai dai manoman da aka tasa daga wajen sun koka kan yadda aka fidda su daga wajen.

Margaret da yanzu haka ke zaune a kauyen Kitembo na daga cikin wanda aka tasa daga inda gonakinsu suke shekaru 12 da suka gabata batun da ya sanya ita 'ya'yanta komawa wani gida na katako da ta ke biyan hayar dalar Amurka 15 a wata daura da gonar Coffee ta Kweri, batun da ya sa ta ce ta na cikin wani mawuyacin hali don bata da wata hanya tsayayya ta samun kudin shiga, kazalika mijinta da ke aiki a gonar kofin ta Kweri na samun kwatankwacin dalar Amurka daya da rabi ne kawai a kullum.

Margret ta ce "muna shan wuya domin a gidajen haya muke kuma bamu da gonakin da za mu yi noma. Wasu daga cikin abokan aikinmu sun samu gonaki daga gonar Coffee din inda nan ne muke samu mu hayi 'yar gayauna don noma dan abin da za mu ci."

Bildergalerie Bioanbau in Uganda Wildkaffee

Noman Coffee a Uganda ya koma hannun yan kasashen ketare

Ba wai Margret ce kadai ke fuskantar wannan matsala ba, sauran mutanen yankin ma sun shiga wannan hali, inda gwamnatin kasar ta yi alkawarin biyansu diyyar gonakinsu sai dai har yanzu babu wani abu da gwamnatin Ugandan ta yi kamar yadda John Bosco Senginiya wani lebura a guda daga cikin gonakin yankin ke bayyanawa.

Ya ce "ban samu ko da shillin dari na kudin Uganda ba sai ma dai dukan kawo wuka da na sha. Dukan da suka yi mana shi ne irin tsarin biyansu. Shin sun san nawa ma ya kamata a biyamu?"

To sai dai yayin da John ke wadannan kalamai, kamafanin Neumann Gruppe na kasar Jamus wanda shi ne ke amfani da gonakin mutanen da aka tasa ya ce gwamnatin Uganda ta biya diyya ga iyalai 166 wanda daga bisani suka tashi daga wajen yayin da iyalai 25 suka ki tashi, batun da ya sanya gwamnatin kasar tashinsu da karfin tuwo.

To da ya ke kamfanin na kasar ta Jamus da ke aiki yanzu haka a wannan yanki ya ce gwamnatin Uganda ta biya masu gonaki kafin a tashe su, DW ta tuntubi wasu daga cikin mazauna kauyen ko nawa aka basu a matsayin diyya ta gonakinsu.

Guda daga cikin kauyawan ya ce ya danganta da girman gonar mutum amma dai ya ce ba su san yadda tsarin diyyar ya ke ba.

Ita kuwa wata mata cewa ta yi lissafa abinda mutum ke da shi suka ce za su yi sai su bashi diyya daidai da abinda ke ya mallaka.

Präsident von Uganda Yoweri Museveni

Shugaban Uganda Yoweri Museveni

To sai dai duk da wadannan hali da mutanen wannan yanki da ke gundumar Mubende a tsakiyar kasar ta Uganda suka shiga bayan rasa gonakinsu, yankin na bunkasa a hankali amma ana fuskantar kalubale da dama da suka hada da makamashi da tsabtattace ruwan sha duk kuwa da cewar kamfanin da ke aiki a wajen ya samar da ruwan famfo.

Wannan ne ma ya sanya wasu daga cikin mazauna yankin bayyana ra'yinsu kan yadda rayuwa zata kasance nan gaba.

Wata mata da ta zanta da DW ta ce ''haka dai abubuwa za su cigaba da kasancewa ba tare da yaranmu sun samu ilimi mai nagarta ba''

Shi kuwa wani mutum cikin fushi cewa ya yi ''magana ta gaskiya ban san yadda zata kaya ba. Ban sani ba ko abubuwa za su cigaba da kasancewa yadda su ke ko akasin haka''

To ma dai ya lamura za su kasance a wannan yanki, lokaci ne kawai zai yi alkalanci.