Kano: Tallafawa marasa lafiya | Himma dai Matasa | DW | 22.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Kano: Tallafawa marasa lafiya

Kungiyar Iyalan Gidan Na’abba, saboda yawan marasa lafiya da ake samu a cikin birnin Kano da kewaye, ya sa suka tara gudunmowar da suka sayi magunguna tare da gayyato likitoci don su duba marasa lafiyar unguwarsu


  Daruruwan  mutane ne  suka hallara a kofar hidan  Alhaji Sule Na’abba a dogon lungu, a ranakun Asabar da Lahadi don a binciki cututtukan da suke fama da su a kuma basu magunguna kyauta a cewar  Mal Abubakar  Na’abba jagoran shirin kula da lafiyar al’umma da kungiyarsu ta kirkira.


"Ko ina mutum ya zo idan dai ba ka da lafiya za a duba ka abin da ya sameka kama daga  harkar da ta fi shafar Malaria hawan jini  Typhoid da kuma sanyi da ya fara shigowa dinnan,  ciwon sugar  akwai abin da za mu ce har da shi ba,  shi ma ana dubawa sai a ba su shawarwari su tafi asibiti lokaci kaza. To wannan a kan tsarin  ake kuma har  ya zuwa yanzun nan  da muke aikin  abin ya ninka ma na jiya."
       

Duk da cewa Gwamnatin Kano ba ta gaza ba ta bangaren kula da lafiyar, amma a cewar Malam Abubakar hannu da yawa ne zai iya maganin kazamar miya.

 

"Idan dai za' a tsaya a taimaka a dubi al’umma wallahi gwamnati ma babu ruwanmu da ita.A junanmu ma za mu iya zama gwamnati mu tsara al’ummarmu  al’amuran  da zasu ji dadi. Domin wannan ya nuna mana danba domin  ko yanzu  said a wani likita ya gaya mana tuni har sun fara shirin wata unguwa zasu yi irin wannan tsarin namu da muka yi".