1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kanada za ta tabbatar da dokar halasta shan wiwi

Ramatu Garba Baba
October 12, 2018

A wannan juma'ar a hukumance kasar Kanada za ta tabbatar da dokar halasta sayar da shan ganyen wiwi. Daga ranar 17 na wannan watan za a soma noma ganye ko shan tabar don nishadi a bainar jama'a.

https://p.dw.com/p/36PfD
Deutschland Drogen - Drogenkonsum
Hoto: picture alliance/dpa/T. Leukert

A watan Yunin da ya gabata ne 'yan majalisar wakilai a kasar suka kada kuri'ar amincewa da dokar. Dokar ta sha fuskantar suka inda masu adawa da ita, suka soki matakin a sanadiyar illar da za ta yi ga rayuwar jama'a musanmman matasa. Amma alfanun amincewa da dokar ta fuskar bunkasa tattalin arziki ya danne korafin da masu adawan ke yi da ita.

Hasali ma yana daga cikin alkawuran da Firaiminista Justin Trudeau ya yi a lokacin yakin neman zabensa na zartas da dokar muddun ya yi nasara.