1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rabuwar kan adawa kafin zaben Kwango

Yusuf Bala Nayaya
November 12, 2018

Babbar jam'iyyar adawa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta yi fatali da yarjejeniyar da aka cimma ta zaben dan takara guda daya tilo da zai jagoranci bangaren jam'iyyun adawa a zaben shugaban kasa da za a yi a kasar.

https://p.dw.com/p/387w2
DR Kongo Trauer um Etienne Tshisekedi
Felix Tshisekedi sanye da jar riga a tsakiyar 'yan adawar KwangoHoto: Reuters/R. Carrubba

Bayan da 'yan fafutika da dama suka gudanar da zanga-zanga Jean-Marc Kabund babban sakataren jam'iyyar ta UDPS ya bayyana cewa 'yan jam'iyyarsu tun daga tushe sun bukaci Felix Tshisekedi ya janye daga wannan yarjejeniya sun kuma bashi sa'oi 48 ya aikata haka.

Shugabannin 'yan adawa bakwai ne suka gana a ranar Lahadi inda suka zabi mutumin da bai zama fitacce ba Martin Fayulu a matsayin wanda zai daga tutar kawancen adawa a zaben da aza a yi ranar 23 ga watan Disamba.