1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karayar arziki ta sami kamfanin Thomas Cook

Abdullahi Tanko Bala
September 23, 2019

Kamfanin zirga zirgar fasinjoji mafi girma a duniya Thomas Cook ya sanar da samun karayar arziki bayan da ya kasa cimma yarjejeniya da masu zuba jari a kokarin ceto shi daga durkushewa.

https://p.dw.com/p/3Q4kQ
Pauschaltourismus Thomas Cook Flugzeug
Hoto: picture alliance/empics/T. Goode

Kamfanin dai na neman kimanin fam miliyan 200 kwatankwacin euro miliyan 227 daga yan kasuwa masu zaman kansu domin tsamo shi daga durkushewa amma lamarin ya faskara.

Wannan dai ya haifar da gagarumin aikin dawo da dubban fasinjoji gida wanda ke zama hidima mafi girma tun bayan yakin duniya na biyu.

Rahotanni sun ce matakin ya bar fasinjoji yan yawon bude idanu kimanin 600,000 a fadin duniya wadanda ke neman a dawo da su gida.

Kamfanin wanda ya shafe shekaru 178 yana aiki ya fuskanci kalubale daga kamfanoni da ke gudanar da hulda ta yanar gizo. Ana danganta rashin samun matafiya ga kamfanin ga halin rashin tabbas na shirin ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai.

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar da safiyar yau Litinin yace duk da iya kokarin da ya yi an kasa cimma matsaya tsakaninsa da masu hannun jari da kuma sabbin masu zuba jarin.