Tattalin arziki
Kamafanonin Fiat da Peugeot sun hade
December 19, 2019Talla
Sabon kamfanin hadin gwiwar zai kunshi ma'aikata dubu 400 ,sannan karfin hannun jarinsa zai kai miliyan dubu 170 na Dalar Amirka da kuma sayar da motoci milian takwas da dubu 700 a kowace shekara.
Kamfanonin biyu sun ce suna sa ran aikin karkare hadewar tasu a waje daya zai dauki watanni 12 zuwa 15 daga yanzu. Kamfanin kera Motoci na Volkswagen na kasar Jamus ne dai ke a yanzu haka a sahun gaba wajen sayar da motoci a duniya.
Kamfanin hadin gwiwar Faransa da Japan na Ranault-Nissan- Mitsubishi na a matsayin na biyu a yayin da kamfanin Toyota na kasar Japan ke a matsayin na uku.