Kamen masu zanga-zanga a Hong Kong | Labarai | DW | 26.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamen masu zanga-zanga a Hong Kong

A yammacin jiya Alhamis wasu masu zanga-zangar kusan 300 sun fito cibiyar kasuwancin lardin Mongkok inda suka fafata da ‘yan sanda cikin sa’oi biyar.

A kalla mutane 44 aka kama bayan sake wata fitowar masu zanga-zangar kafa dimokradiya sahihiya a Hong Kong kamar yadda rahotanni suka nunar a yau Juma'a.

Masu zanga-zangar dai sun fara tattaruwa a ranar Laraba a cibiyar kasuwancin lardin Mongkok da ke mashigar teku Kowloon inda a ranar aka kama mutane 12 kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.

A yammacin jiya Alhamis kuma wasu masu zanga-zangar kusan 300 sun fito inda suka fafata da ‘yan sanda cikin sa'oi biyar a dai wannan yanki, tare da furta kalaman neman kafa dimokradiya kamar yadda jaridar South China Morning Post ta shedar.

‘Yan sanda sun kama maza ashirin da mata goma saboda laifin lalata wasu abubuwa a yankunan gidajen jama'a a yankin haka zalika an kuma kamo wasu mutane biyu saboda alka da zanga-zangar.