Kamen jami'an FIFA a Switzerland
May 27, 2015
An tsare wasu jami'an hukunmar kwallon kafa ta duniya FIFA a Switzerland in da za a tisa keyarsu zuwa Amirka saboda zargin wata almundahna ta cin hanci da rashawa.
Ofishin shari'a na kasa a Swiss ya bayyana cewa an tsare jami'ai shida daga hukumar ta FIFA inda za a ci gaba da dakon ji daga bangaren Amirka ko za ta bukaci a mikasu gareta kafin babban taro da hukumar ta FIFA ta tsara yi a Zurich.
A bayanan da ofishin shari'a na kasar ta Switzerland ya fitar a ranar Laraban nan, ya nunar da cewa jami'an Amirka na zarginsu da karbar cin hanci na makudan miliyoyin daloli.
Ya ce ofishin mai shari'a a gabashin New York na gudanar da bincike kan wadannan jami'ai inda ake samun hannunsu a badakalar cin hanci da rashawa tun daga shekarun 1990 zuwa yanzu.
Ita ma dai Amirkar a yanzu ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan wadannan jami'ai.