Kame Saddam Hussein | Siyasa | DW | 15.12.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kame Saddam Hussein

A farkon watan afrilun da ya wuce ne tsofon shugaban kasar Iraki Saddam Hussein ya bayyana a hukumance a bainar jama'a, jim kadan kafin sojan Amurka su mamaye birnin Bagadaza. Tun daga wannan lokaci Saddam ya zama tamkar fatalwa aka rasa makomarsa. An yayata maganar mutuwarsa, amma daga baya sai ga jawabai da ya rika gabatarwa ta kaset-kaset yana mai kira ga al'umar Iraki da su nuna juriya. An samu wasu dake ikirarin cewar shi ne mai alhakin shirya hare-haren da ake kaiwa kan sojan mamaye a Iraki, a yayinda wasu suka yi tsammanin cewar tuni hambararren shugaban tuni ya tsallaka zuwa Amurka sakamakon wata daidaituwar da aka cimma da fadar mulki ta White House a asurce. A yanzun dai dukka wadannan jita-jita da tsinci-fadi ba su da sauran alfanu, musamman ma ga masu tababa. An kame Saddam Hussein a Tikrit, garinsa na haifuwa. Mai yiwuwa kame shi da aka yi ya kasance wani mataki mai muhimmanci dangane da makomar kasar Iraki. Domin kuwa daga bisanin nan ne aka ba da sanarwa a game da kafa wata kotu da zata ci shari'ar masu laifukan yakin Iraki kuma ga alamu tsofon shugaban ne zai zama wani fursina mafi muhimmanci da kotun zata ci shari'arsa. Domin kuwa Saddam Hussein shi ne ya fi kowa alhakin ta'asar da ta rutsa da al'umar kasar ta Iraki da wadda ta shafi makobtanta tun abin da ya kama daga shekarun 1960. Kuma ko da shi ke daga bisani an lura da cewar ba tsofon shugaba Saddam Hussein ne ke da alhakin hare-haren da ake kaiwa kan sojan Amurka da kawayenta ba, amma al'umar kasar na dada kaurace wa sojojin mamayen sakamakon gazawar da suka yi na kame hambararren shugaban. Kazalika, ko da yake zai zama ragon azanci a yi zaton cewar tun daga yanzu za a dakatar da matakan hare-haren kan sojojin taron dangin, amma mai yiwuwa kamewar ta taimaka magoya bayan Saddam Hussein su hakikance cewar ba zai sake komawa kan karagar mulki ba su kuma canza salon tunaninsu a game da matakansu na adawa. Bugu da kari kuma a yanzu al'umar kasar zasu daina fargabar cewa idan sun ba wa sojan Amurka hadin kai nan gaba za a fatattakesu a matsayin masu cin amanar kasa. A yanzu wannan barazana ta kau kuma ba abin da ya rage illa al'umar Iraki su dauri wata sabuwar niyya ta kyautata makomar kasarsu a karkashin wani kyakkyawan yanayi na zaman lafiya da cude-ni-in-cude-ka da juna.