Tashin hankali na kara yin muni a Kamaru
March 8, 2020Talla
Tun can da farko 'yan Ambazonia sun gargadi jama'a da ka da su fito a bikin ranar duniya ta mata da ya gudana (08-03-20) kafin cikin dare a kwahe sa'oi ana yin dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin da na 'yan awaren. Wakilin DW Baba Abdullahi ya ce 'yan awaren sun tayer da bam kirar gargajiya a tsakiyar garin wanda yanzu haka aka samu asarar dukiyoyi da kadarori, sai dai ba a tantance ba asarar.