Kama sojojin ruwan Rasha a Lagos | Labarai | DW | 23.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kama sojojin ruwan Rasha a Lagos

Hukumomin Tarayyar Najeriya sun kama jirgin ruwan Rasha tare da cafke matukanta 15 bisa zargin safarar muggan makamai a ruwan Lagos da ke kudancin kasar.

(FILES) File photo dated on September 11, 2007 shows the Murtala Muhammed International Airport in Lagos. Nigeran Umar Farouk Abdulmutallab, 23, was subdued by fellow passengers and crew aboard a Northwest Airlines flight from Amsterdam on December 25, 2009 after he allegedly tried to detonate an explosive device as the plane descended toward Detroit. Dutch authorities confirmed that the detained suspect had flown from Nigeria to Amsterdam and then on to Detroit with a valid US visa. Nigerian officials said on December 26, 2009 that he had boarded a KLM flight from Lagos after undergoing normal security checks at the airport. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)

Filin tashi da saukan jiragen sama na Lagos

Hukumomin Tarayyar Najeriya sun cafke wasu 'yan Rasha 15 bayan da suka gano makamai masu tarin yawa da kuma albarusai 8500 a jirgin ruwan da ke dauke da su. Kakakin rundunar sojojin ruwan Najeriya Commodore Aliyu Kabiru ya ce tun a karshen mako ne suka yi nasarar bankodo sirri jirgin ruwan na Moscow a gabar ruwan Lagos. Wata majiya da bato so a bayyana sunanta ba ta ce daga cikin makamai da a gano har da bindigo da ke sarrafa kansu da kansu.

Fashin teku da safarar miyagun makamai na dada samun gindin zama a ruwan Najeriya a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tsaro da kuma fashe fashen bututan mai a yankin Niger Delta. 'Yan fashi na amfani da tekun Lagos wajen jigilar makamai ba bisa ka'idama zuwa wasu sassa na yammacin Afirka da ma dai duniya baki daya.

A shekara ta 2010 ma dai dangantaka ta yi tsami tsakanin Tarayyar ta Najeriya da Iran bayan da ta gano makaman da aka zargi hukumomin Teheran ke kai wa 'yan tawayen Casamance na kasar Senegal.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu