Kalubalen Kenyatta, shekara guda a kan mulki | Siyasa | DW | 09.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kalubalen Kenyatta, shekara guda a kan mulki

Shugaban na Kenya dai ya gaza cikanta alkawura da ya dauka na hada kan al'umma da samar wa matasa aiki da bunkasa tattalin arziki da sashin ilimi a Kenya.

A ranar 9 ga watan Afrilun shekara ta 2013 dai Uhuru Kenyatta ya yi rantsuwar karbar mukamin shugaban Kenya, inda nan ta ke ya yi wa al'ummar kasar alkawura masu yawa da suka hadar da bunkasa tattalin arziki, hadin kan al'umma, biyan kudaden kiwon lafiya, bunkasa abinci , samarwa matasa aikin yi, da kuma kwamputa na laptop wa dukkan daliban makarantun framare.

To sai dai bisa dukkan alamu kalilan daga cikn wadannan alkawura aka cimma. Farashin kayayyakin abinci dai sun yi tashin gwauron zabi a Kenya, a yayin da babu sauyin zani dangane da yawan matasa da ba su da aikin yi, batun laptops wa yaran makarantun framare kuwa ya yi batan dabo tun bayan wata badakkar cin hanci da aka bankado kan wannan shiri. A cewar Inchikirwa Ndelejai da ke zama 'yar jarida a kasar ta kenya dai da sauran rina a kaba:

" Babu wani abun a zo a gani da gwamnati ta yi. Domin basu cikanta alkawuran da suka dauka ba. Matsalar ita ce sun dauki alkawura masu yawa, wadanda idan muka kwatanta alkawuran da abun da ke a zahiri, zan ce babu abun kirki da suka yi".

Nairobi Explosion Anschlag 30.4.14

Kalubalen tsaro a Nairobi

Sai dai Kenyatta ya kafa tubalin aiwatar da daya daga cikin alkawura da ya dauka da hawansa kan kujerar mulki. Mata masu juna biyu a Kenyan dai yanzu haka na samun kulawa kyauta har zuwa haihuwa. A jawabinsa gabannin bukin cika shekara guda kan karagar mulki, shugaban na Kenya ya yi ikirarin irin nasarori da kasar ta samu a fannin bunkasar tattalin arziki da yaki da cin hanci da karbar rashawa. Sai dai a zahiri ba haka lamarin ya ke ba, kamar yadda shugabar ofishin gidauniyar Heinrich-Böll da ke Kenya Katrin Seidel ta nunar:

"Akwai yanayin da hukumar binciken ke samun wasu manyan jami'an gwamnati da laifi a sashin tsaro ko kuma na 'yansanda, amma zasu cigaba da rika mukamiansu na gwamnati".

Ba wai a fannin cin hanci da rashawa ne mafi yawa daga cikin al'ummar kasar suka yi kasa a gwiwa da sashin tsaron kasar ba, har ma da batun harin da aka kai a cibiyar cinikin nan na Westgate da ke birnin Nairobi a bara. Idan za'a iya tunawa dai, a ranar 21 ga watan satumban shekara ta 2013 ne dai, mayakan sakai na Al-Shabaab na kasar Somaliya suka yi wa cibiyar da ke cike da masu saye da sayerwa kofar rago, inda masu harin suka yi garkuwa da mutane na tsawon kwanaki hudu. Bayan wannan hari ne dai al'ummomin kasar ta Kenya suka fara shakku dangane da ko gwamnati za ta iya basu kariyar da suke bukata. Sai dai Kenyatta ya sake jaddada manufar gwamnatinsa na kare al'umma:

Internationaler Strafgerichtshof Anhörung

Kotun kasa da kasa ta ICC

" Kare lafiyar al'ummar da martabarsu na daga cikin hakkoki da suka rataya a wuyana. Ba zaku kasance cikin wata fargabar barazana ba, duk wanda ya taba mu zai ci karo da martani".

Kotun kasa da kasa da ke hukunta masu manyan laifukan ta ICC da ke birnin The Hague na kasar Netherlands dai, na zargin shugaban na Kenya da mataimakinsa William Ruto da hannu a rikicin da ya barke bayan zaben watan Disamba shekara ta 2007.

Mafi yawan al'ummomin Kenyan dai basu gamsu da gwamnatin Uhuru Kenyatta ba. Bisa la'akari da dumbin kalubale dake gabanta, kuma babu alamun zata sauya zani.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Muhammad Nasir Awal

Sauti da bidiyo akan labarin