Kalubalen fitar da dan takarar shugabancin Najeriya a APC | Siyasa | DW | 09.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kalubalen fitar da dan takarar shugabancin Najeriya a APC

Bayyana cewa janar Buhari zai tsaya takara a zaben share fage na neman shugaban kasa a sabuwar jam'iyyar adawa ta APC ya haifar da sabuwar takaddama.

Sabon zubi na jam'iyyar adawa ta APC da ta zo cike da sabuwar fata da ma bada wani zabi ga al'ummar Najeriya, musamman ma dai 'yan adawan kasar. To sai dai yadda jam'iyyar za ta bullo wa batun dan takarar shugaban kasa, na daya daga cikin abin da ke tsolewa mutane da dama ido, da ya zama babban kalubalen da ke gaban jam'iyyar.

To sau uku a jere dai ana fafatawa da janar Muhammadu Buhari a takarar da ya yi ta neman zama shugaban Najeriyar ba tare da samun nasara ba, a zabubbukan da suka kasance cike da zargin tafka magudi da ma tababar sahihancinsu.

Wannan kalubale da ya kara bayyana a fili, sanin cewar wane ne janar Muhammadu Buhari a fagen siyasar Najeriyar, ya sa malam Buhari Muhammad Jega na cibiyar nazarin dimokradiyya da ke Abujan Najeriya, bayyana cewar, akwai bukatar yin taka tsan-tsan da wanan batun domin kaucewa a fasa kowa ya rasa:

"Na farko in ka duba shi janar Muhammadu Buhari a matsayinshi na dan takara, sau uku ko ma na hudu kenan zai shiga. Eh, yana da jama'a kuma mutane suna nuna dabio'i masu kyau da sauransu, amma dabio'i daban kuma cin zabe daban. Duk maganar da a ke a Najeriya a yanzu, mutane suna neman mafita ne, suna neman wane ne wanda zai fitar dasu daga kangi da halin da dimokradiyya ta shiga. Don haka lallai sai ita jam'iyyar nan ta yi nazari a kan shin wane ne wanda za ta fitar ma a matsayin dan takarar shugaban kasa."

Supporters of leading opposition leader Muhammadu Buhari of the All Nigeria People's Party (ANPP), run against a backdrop of the Legislature and Aso Rock at a party rally in the Nigerian capital Abuja Tuesday, April 8, 2003. The rally in support of Buhari and his running mate Chuba Okadigbo was held ahead of the upcoming general elections to be held on Saturday, April12, 2003 and presidential elections on Saturday, April 19, 2003. (AP Photo/Ben Curtis)

Magoya bayan janar Buhari

Matsayin Buhari a sabuwar jam'iyyar APC

A yayin da babu wanda ya fito fili ya nuna ja da duk wani yunkurin da Janar din ke yi a batun takara a 2015, musamman tun daga lokacin da ya bayyana cewa zai ci gaba da takara a fagen siyasar Najeriyar, domin abin da ya bayyana da kawar da zalunci a kasar, to amma ga Honourable Faruq Adamu Aliyu, jigo a jam'iyyar ta APC, ya ce a yanzu dai muhimman abin da suka sanya a gaba shi ne zaben shugabannin sabuwar jam'iyyar, domin zaburar da ita cikin harkar siyasar Najeriyar, don haka suke hanzarin hakan:

"Zamu yi kokari a cikin watanni uku a yi wannan zabe na shugabannin jam'iyya domin abin da dokar zabe ta ce shi ne, sai zababbun shugabannin jam'iyya ne kadai za -su iya fitar da zaben fid-da-gwani a jam'iyya. Akwai zabe mai zuwa a jihar Anambra wannan zabe, a dalilinsa za mu yi iya kokarinmu mu fitar da shugabanni, wanda za mu yi hakan ko don jihar Anambra mu gwada karfinmu kafin 2015."

Nigerians line up to cast their votes for the General Election in Abeokuta, 50 miles north of Lagos, Saturday, April 12, 2003. Abeokuta is the home town of President Olusegun Obasanjo who cast his vote there in the morning. (AP Photo/Ben Curtis)

Karbuwar da Buhari ke da ita a fagen siyasa

Karfi, ko sahihancin jam'iyyar adawa a Najeriya dai, na zama muhimmin batu da masana dimokradiyya ke zuba ido domin ganin kama rawar jam'iyyar ta APC da a yanzu ke zama wacce ake hasashen barazanarta ka iya yiwa jam'iyyar PDP da ta kwashe fiye da shekaru 14 tana mulki illa. To, sai dai ga malam Abubakar Umar Kari, masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abujan Najeriya, ya ce yana kallon batun takarar Buhari ne ta bangarori biyu. To amma, anya APC ma za ta iya samar da adawar da a ke bukata kuwa?

"Kwarai kuwa, za ta iya kuma ana kyautata zaton za ta yi hakan, amma dai Buhari zai iya kasancewa nasara ko rashin nasarar jam'iyyar APC. Wannan ya danganci yadda suka yi da shi sha'anin Buhari. Zai kasance wauta idan har jam'iyyar APC basu sarrafa karbuwar da yake dashi a yankin arewacin Najeriya ba. Ta wani bangare kuma, Buhari bashi da karbuwa a jihohin kudancin Najeriya, kuma a iya cewa wannan ya hanashi samun nasara a zabubbukan uku da ya tsaya. Saboda haka, takarar Buhari kamar wani zakaran gwajin dafi ne."

Koma dai wane kauce-kauce jam'iyyar ta APC ke yiwa batun dan takarar neman shugabancin kasa a jam'iyyar, a zaben na 2015 a bayyane take cewa, wannan batu ne mai sarkakiyar gaske da baya ma ga muhimancinsa, zai ci gaba da kasancewa babban kalubalen da ke gaban jam'iyyar da ke daura damarar fuskantar fagen siyasar Najeriyar.

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin