Kalubale ga kungiyar ′yan uwa Musulmi | Labarai | DW | 01.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kalubale ga kungiyar 'yan uwa Musulmi

Birtaniya ta bukaci a gudanar da bincike kan kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Masar bayan da aka samu rahotannin cewa ta koma da shelkwatarta birnin London na Birtaniyan.

Firaministan Birtaniya David Cameron ne ya bukaci hukumar tsaron kasar da ta gudanar da bincike a kan kungiyar ta 'yan uwa Musulmi ta Masar din bayan da aka ce ta koma da gudanar da ayyukanta a birnin London biyo bayan matsa musu lamba da mahukuntan Masar din ke yi. Ofishin Firaminista Cameron ne ya sanar da hakan inda ya ce tuni ya kaddamar da kwamitin cikin gida domin ya gudanar da bincike a kan kungiyar 'yan uwa Musulmin ta Masar da kuma kudirin gwamnati a kan kungiyar. A shekarar da ta gabata ta 2013 ne dai sojoji suka kifar da gwamnatin hamabararren tsohon shugaban kasar Masar din kuma daya daga cikin jiga-jigan kungiyar ta 'yan uwa Musulmi Mohammed Morsi yayin da kuma mahukuntan kasar na yanzu suka ayyana kungiyar a matsayin ta 'yan ta'adda tare kuma da kokarin murkushe ta da karfin tuwo. Kungiyar dai ta musanta cewa tana da alaka da ayyukan ta'addancin ta mahukuntan Masar din ke zargin ta a kai.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane