1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fayulu ya ce zai je kotu kan zaben Kwango

Mohammad Nasiru Awal YB
January 11, 2019

Yayin da Martin Fayulu ya ce za shi kotu, hukumar zaben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya goyi bayan sabbin shugabannin kasar bayan manyan kasashe na sukar zaben.

https://p.dw.com/p/3BQND
DR Kongo nach Wahlen Martin Fayulu Anhänger
Hoto: Reuters/B. Ratner

Wannan kiran na zuwa daidai lokacin da mutumin daya zo na biyu a zaben Martin Fayulu ya ce zai kalubalancin sakamakon zaben a gaban kotu. Martin Fayulu hamshakin dan kasuwa da ya yi suna wajen sukar matsalar cin hanci da rashawa da ta zama ruwan dare a Kwango, ya fada wa daruruwan magoya bayansa da suka hallara a Kinshasa babban birnin kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango cewa ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar na ranar 30 ga watan Disambar 2018, da hukumar zaben kasar CENI ta ce Felix Tshisekedi ne ya lashe. Fayulu ya ce a ranar Asabar za su yi gangami a gaban babbar kotun kasar.

Bildkombi: Präsidentschaftskandidaten für die bevorstehenden Wahlen in der Demokratischen Republik Kongo
'Yan takara uku sun zama taurari yayin zaben na KwangoHoto: Reuters/K. Katombe / B. Ratner / S. Mambo

Kasar Faransa da kasar Beljiyam wadda ta yi wa Kwango mulkin mallaka, sun saka ayar tambaya game da sakamakon zaben, yayin da kasar Amirka ta yi kira da a yi cikakken bayani bayan da majami'ar Katholika da ta tura jami'an sa idon zabe su kimanin dubu 40, ta ce sakamakon da hukumar zaben Kwango wato CENI ta sanar bai yi daidai da wadanda jami'anta suka tattara ba. Didier Reynders shi ne ministan harkokin wajen kasar Beljiyam da ya ce kasarsa na sa ido kan abin da ka iya faruwa a Kwango, kuma kasar na aiki kan wani shiri na kare baki matukar rigima ta barke a Kwango.

Unruhen im Kongo
Zaman rashin tabbas ba bako ba ne a KwangoHoto: Getty Images/AFP/J. Wessels

Ita dai hukumar zaben a Kwango wato CENI ta ayyana daya daga cikin 'yan takarar 'yan adawa Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben, sai dai Emerie Damien Kawira shugaban kawancen wani gungun 'yan siyasar Kwango mai mazauni a birnin Brussels na kasar Beljiyam ya ce akwai wani shiri a boye tsakanin Shugaba Joseph Kabila da Tshisekedi.

Idan aka tabbatar da sakamakon, to zabe zai zama irinsa na farko da za a mika mulki ta hanyar dimukuradiyya a Kwango.