1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Nijar da 'yan adawa

August 12, 2014

A daidai lokacin da gwamnatin haɗin kan ƙasa ta Nijar ta cika shekara guda, wacce 'yan adawa suka ƙaurace mata, har yanzu ba a ga maciji tsakanin sassan biyu.

https://p.dw.com/p/1Ct7s
Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou da Hama Amadou shugaban majalisar dokokiHoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

A cikin watan Augusta na shekarar bara ne shugaban ƙasar Nijar Mahamadou Issoufou ya nemi haɗin kai na dukkanin 'yan siyasa na ƙasar domin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa. Abin da shi ne dalili na farko da ya janyo ruɗanin siyasar da ake fama da shi a ƙasar.

'Yan adwa na zargin gwamnatin da haddasa fitina a cikin jam'iyyun siyasunsu.

Ko shakka babu tsofin abokanan ƙawancen jam'iyyar PNDS Tarayya mai yin mulki watau Modem Africa Luma ta kakakin majalisar dokokin Nijar Hama Amadou. Ita ce jam'iyya ta farko da ta fice daga ƙawancen bayan da gwamnatin ta naɗa wasu magoya bayan jam'iyyar a matsayin ministoci ba tare da amincewar jam'iyyun ba, kafin daga bisanin jam'iyyar MNSD Nasara ita ma ta ce an yi mata irin wannan surkule.

Omar Hamidou Tchiana, Minister für Bergbau und Industrielle Entwicklung von Niger
Omar Hamidou Tchiana ɗaya daga cikin manbobin kwamitin gabatarwa na jam'iyyar Lumana wanda ya canza sheƙa ya karɓi matsayin minista.Hoto: DW/M. Kanta

Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam na zargin gwamnatin da karya dokokin demokaraɗiyya.

A tsawon shekara guda gwamnatin ta Nijar ta yi ta kai ruwa rana da 'yan adawar da 'yan makaranta da 'yan jaridu da kuma wasu jam'ian ƙungiyoyin farar hula. Yazuwa yanzu dai gwamnatin na tsare da wasu 'yan siyasar da 'yan makarata da dama waɗanda ta ke zargi da laifukan haddasa fitina a cikin ƙasar. Matakin da wasu masu yin sharhi a kan al'ammura ke ganin cewar wani yunƙuri ne na gwamnatin na murƙushe duk wani wanda ya ce zai ƙalubalanceta.

Sitzung des Parlaments in Niger
'Yan majalisun dokokin NijarHoto: DW/M. Kanta

Mawallafi: Larwana Malam Hami
Edita : Zainab Mohammed Abubakar