Kagame ya na niyar yin tazarce a Ruwanda | Labarai | DW | 20.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kagame ya na niyar yin tazarce a Ruwanda

Majalissar dokokin ta fara sauraren ra'ayin jama'a kan matakin yin kwaskwarima ga kundin tsarin milkin kasar domin bawa shugaba Paul Kagame damar yin tazarce

Majalissar dokokin kasar Ruwanda ta soma aikin sauraren ra'ayoyin jama'a a fadin kasar dangane da matakin yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar domin bawa Shugaba Paul Kagame damar sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa na shekara ta 2017. 'Yan majalissar za su share makonni uku suna rangadin jin ra'ayin jama'a a duk fadin kasar.Tun 14 ga wannan wata na Yuli ne dai majalisar dokokin kasar ta Ruwanda ta amince da wannan mataki lokacin wani zama da ta gudanar.

Sai dai wasu masu lura da yanayin tafiyar siyasar kasar ta Ruwanda na ganin wani cikon sunna ne dai kawai za a yi domin tun ma kafin majalisar dokokin kasar ta amince da shirin 'yan kasar ta Ruwanda kusan miliyon hudu ne suka sanya hannu a kan wata takardar neman amincewa da matakin yin kwaskwarima domin bawa shugaba Paul Kagame damar yin tazarce.