Kagame na Ruwanda na neman yin tazarce | Labarai | DW | 16.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kagame na Ruwanda na neman yin tazarce

Jam'yyar FPR ta Paul Kagame ta bayyana goyan bayanta ga matakin yi wa kundin tsarin milkin kasar kwaskwarima domin bashi damar yin tazarce a 2017

A Kasar Ruwanda jam'iyyar FPR ta shugaba Paul Kagame ta bayyana goyan bayanta ga matakin neman yin kwaskwarima ga kundin tsarin milkin kasar domin bai wa shugaban damar sake tsayawa takara a karo na ukku a zabe mai zuwa na 2017.

Hukumomin kasar ta Ruwanda dai na cewa wannan shawara da ta fito ne daga wakillan al'umma da shugabannin kungiyoyi daban daban kuma hakan ke nuni da cewa al'umma na goyan bayan shirin tazarcen shugaban mai ci a yanzu.To amma masu adawa da matakin na ganin gwamnatin ce ta kitsa wannan, a wani mataki na neman halitta wa Paul Kagame wanda ke rike da ragamar milkin kasar tun a shekara ta 1994 haramtacciyar aniyarsa ta neman dawwama akan milkin kasar.

Nan zuwa hudu ga watan Ogusta mai zuwa ne Majalissar Dokokin Kasar ta Ruwanda za ta bayyana matsayinta akan wannan mataki.