1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kabul:Harin kunar bakin wake a farkon azumi

Abdourahamane Hassane
March 27, 2023

A Afghanistan wani harin kunar bakin wake da aka kai kusa da ma'aikatar harkokin wajen kasar da ke a birnin Kabul, ya yi sanadiyyar mutuwar fararan hula guda shida, yayin da wasu goma suka jikata.

https://p.dw.com/p/4PKiW
Afghanistan I Selbstmordanschlag in Kabul
Hoto: Wakil Kohsar/AFP/Getty Images

Maharin wanda jami'an tsaro suka gano yana dauke da makamai suna cikin kokarin kai masa hari, ya tayar da bama-baman da ke a jikinsa. Wannan dai shi ne hari na farko da aka kai a kasar ta Afghanistan tun fara azumin watan Ramadan a ranar Alhamis din da ta gabata. A shekarar da ta gabata an kai hare-hare da dama a daidai irin wannan lokacin na azumin a kasar ta Afghanistan.