1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kabila ya zama wani janar maras sojoji

November 23, 2012

Yankin gabacin Janhuriyar Demokraɗiyyar Kongo ya shafe shekaru masu yawa yana fama da rikice rikice. Hakan na mummunan tasiri ga ci-gaban nahiyar Afirka baki ɗaya.

https://p.dw.com/p/16ok2
Hoto: Peter Busomoke/AFP/Getty Images

A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan rikicin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo. A sharhin da ta rubuta mai taken zamanin Kabila ya kawo ƙarshe jaridar die Tageszeitung ta fara ne da tambayar shin me ne ne abin sha'awa idan a ƙasar Kongo mai fama da rikici sojojin 'yan tawaye suka yi iƙirarin ƙwace wani birni da ke cikin halin na 'yasu? Amsar wannan tambaya tana nuni da makoma maras tabbas ga wani yanki a wannan duniya wanda tun bayan kisan kare dangi da aka yi wa kabilar Tutsi a Ruwanda kimanin shekaru 18 da suka wuce, yake fama da rigingimu da ƙiyayya. Jaridar ta ce Afirka ba za ta iya samun wani ci-gaba ba matuƙar wannan masifa na ci-gaba da wanzuwa a tsakiyar nahiyar, kamar yadda yaƙe yaƙe a Kongo ya nunar. Sai dai jaridar ta ƙara da cewa ƙwace garin Goma da 'yan tawayen M23 suka yi ka iya zama wata dama ga Kongo da ma Afirka gaba ɗaya. Za ta buɗe ƙofar sake yin nazari game da yin muhimman canje canje a wata ƙasa wadda zaman lafiyarta ke zaman sharaɗin ci-gaban Afirka. Dole ne gwamnatin Kongo ta tattauna da abokan gabarta, domin tuni ta rasa abokannen ɗasawa.

Kabila na cikin halin tsaka mai wuya

Kabila ya zama wani janar da ba ya da sojoji inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai cewa sojojin Kongo sun gaza a garin Goma.

Jaridar ta ce mamaye garin Goma hedkwatar lardin arewacin Kivu da 'yan tawaye suka yi na zaman babban cikas ga ƙoƙarin gwamnati a birnin Kinshasa na amfani da rikicin gabacin ƙasar don yin wani mulki na kama karya. 'Yan tawayen sun kusa cimma burin su na matsawa gwamnati ta shiga shawarwari da su duk da cewa a baya shugaba Kabila ya zarge su da zama 'yan korar Rwanda. Kuma duk da cewa sun fi 'yan tawayen na M23 yawa da kuma sanin dubarun yaki, amma sojojin gwamnatin Kongo sun kasa murƙushe wannan bore. Yanzu dai Kabila ya zama wani janar ne maras sojoji, kuma ba zai iya dogaro da sojojin Majalisar Ɗinkin Duniya da ake girke a ƙasar ba, matuƙar 'yan tawayen sun nesanta kansu daga taɓa lafiyar fararen hula. Saboda inji jaridar abin da ya rage wa Kabila shi ne fara tattaunawa da 'yan tawayen M23 da kuma Rwanda.

Goma/ Kongo
'Yan tawayen M23 sun ci ƙarfin sojojin KabilaHoto: Reuters

Afirka na ƙara zama dandalin zuba jari

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a labarin da ta buga mai taken sannu a hankali kamfanonin samar da kayan gine gine na samun ci-gaba a Afirka cewa ta yi:

Kamfanin samar da siminti na Jamus wato Heidelbergcement na faɗaɗa ayyukansa a ƙasashen Afirka kudu da Sahara. Kamfanin dake a matsayi na uku a jerin kamfanonin samar da siminti da duwatsu na fuskantar koma bayan ciniki a 'yan shekarun nan saboda matsalolin karayar tattalin arziki a ƙasashe masu ci-gaban masana'antu. A saboda aka kamfanin ya fara faɗaɗa ayukansa a ƙasashen Afirka inda ake da matuƙar buƙatar siminti. Yanzu haka dai kamfanin na Heidelbergcement yana da masana'antu 13 a ƙasashen Afirka kama daga Saliyo har izuwa Tanzaniya, yana kuma fatan kafin shekarar 2015 zai zuba jari na Euro miliyan 250 don ƙara yawan masana'antunsa a nahiyar Afirka.

Zementwerk
Masana'antar sarrafa siminti na kamfanin HeidelbergcementHoto: picture-alliance/dpa

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu