Juyin mulki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
March 24, 2013Bayan watani hudu na gawgwarmaya, daga karshe dai 'yan tawayen Seleka sun kifar da shugaba François Bozize na Jamhuriya Afrika ta Tsakiya daga karagar mulki.
Kifar da shugaba François Bozize na kama da rama wa kura aniyarta, domin shi ma ta wannan hanya ya zo karagar mulki a shekara 2003, kamin daga bisani a zabe shi ta hanyar demokradiya a shekara 2005.
A watan Disemba na shekara da ta gabata kungiyar tawayen Seleka ta shiga gwagwarmayar kifar da shugaba Bozize wanda take zargi da nakasa tattalin arzikin kasa da kuma jefa al'umma cikin halin kaka ni kayi.Saura kiris Seleka ta shiga babban birnin Bangui,amma bangarorin biyu suka shiga tattanawa a birnin Libreville na kasar Gabon, kuma su ka yi nasara rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ranar 11 ga watan Janairun wannan shekara.
Saidai ba aje ko ina ba,'yan tawayen Seleka suka zargi shugaba François Bozize da rashin mutunta wannan yarjejeniya, domin a cewarsu ya ki belin firsinonin siyasa, sannan ya na ci gaba da rike madafin iko.Bugu da kari 'yan tawayen sun nuna rashin gamsuwa akan cigaba da zaman sojojin Afirka ta Kudu a birnin Bangui.Saboda wannan dalilai da ma karin wasu, su ka yanke shawara sake daukar makamai.Cikin kiftawa da bisimilla, suka yi nasara darkakawa har zuwa fadar shugaban kasa ba tare da fuskantar turjiya mai tsanani ba, duk kuwa da sojojin kasa da kasa da ke jibge a birnin Bangui.
Kakakin kungiyar tawayen Seleka Eric Massi yayi hira ta mussamman da sashen faransanci na DW, inda ya tabbatar da cewar sojojin kasa da kasa ba su tsoma baki ba:
"A iya sani na, babu wasu dakarun kasa da kasa da suka shiga wannan rikici.A yanzu abinda mu ka fi bada fifiko kan sa shine mun maido doka da oda,ko ina cikin kasa, hasali ma mu yaki wanda ke amfani da wannan dama domin kwasar ganima".
Banda sojojin Afirka ta Kudu, da kuma na Kungiyar Kasashen Yankin Tsakiyar Afirka, itama kasar Faransa da ta yi wa Jamhuriya Afrika ta Tsakiya mulkin mallaka, na da daruruwan sojoji, wanda ke gadin filin saukar jiragen sama na birnin Bangui.
A cewar Eric Massi shugaba Bozize kamin ya ranta cikin na kare,saida ya rarraba makamai ga magoya bayansa, domin su cin zarafin jama'a, da zumar bata sunan kungiyar Seleka.
A yayin da aka tambayi Eric Massi game da makomar hambarraren shugaban kasa, cewa yayi:
" A yanzu ba ta Bozize muke ba, abinda ya fi damuwarmu shine mu tabbatar da tsaro a fadin kasa gaba daya, sannan mu sami hanyoyin fuskantar mayan kalubale da ke gabanmu.Allashi daga baya, cikin nutsuwa za mu tunani game da makomar hambarraran shugaban."
A halin da ke ciki dai yanzu rahotani daga Jamhuriya Afrika ta Tsakiya sun ce kura ta fara lafawa, saidai kowa ya shige a gidansa, sannan shaguna sun kasance a rufe.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi