Juyayin hadarin ″Costa Concordia″ | Labarai | DW | 14.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Juyayin hadarin "Costa Concordia"

Shekara guda kenan cur da wani jirgin ruwa mai suna "Costa Concordia" ya samu hadari a tsibirin Gilgio na kasar Italiya

A dangane da haka wadanda suka tsira daga wannan hadari da kuma iyalan wadanda hadarin ya rutsa da rayukansu sun yi wani zama domin nuna alhininsu game da wannan musiba.Daga inda hadarin jirgin ruwan mai tsawon mita 290 ya auku iyalan mamatan da kuma wadanda suka tsira da rayukansu sun jejjefa furanni a cikin teku tare kuma da yin kawaici na miniti guda. Sai da kuma aka yi harbi 32 a cikin iska domin tunawa da mamata. A ranar 13 ga watan Janairun shekaru 2012 ne jigin ruwan mai suna "Costa Concodia" ya ci karo da dutste kusa da tsibirin Toskaniya da mutane 4200 a cikinsu . Mutane 32 cikinsu har da Jamusawa 12 ne suka rasa rayukansu a cikin wannan bala'i.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman